Jummaʼa 2 Oktoba 2026 - 19:01
Jajircewa da Gwagwarmayar Al'ummar Iraki ta Tilasta Sojojin Amurka Ficewa Daga Ƙasar

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Ghafouri, Limamin Juma’ar Kermanshah, ya bayyana cewa Amurka ba don jinƙai ta fice daga Iraki ba, sai dai saboda tsayin daka da juriyar al’ummar Iraki, yana mai cewa irin wannan sakamako na jiran maƙiya a gaban tsayin dakan al’umma.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Kermanshah , Hujjatul Islam wal Muslimin Ghafouri ya bayyana hakan ne a cikin hudubar Sallar Juma’ar wannan mako, inda ya yi kira ga al’umma da kiyaye taƙawa da tsoron Allah, tare da bayyana Sallar Juma’a a matsayin ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin kare lafiyar tunani, aƙida, siyasa da zamantakewar al’umma.

Ya bayyana cewa halartar Sallar Juma’a da yawan jama’a na taimakawa wajen ƙara wayar da kan al’umma da ƙarfafa haɗin kai, tare da kare al’umma daga karkacewar tunani da matsalolin zamantakewa.

Limamin Juma’ar na Kermanshah ya kuma yaba da ayyukan rundunar ’yan sanda wajen tabbatar da tsaron jama’a da ƙasa, yana mai jinjinawa ƙoƙarin jami’an tsaron lardin a lokacin yaƙi da kuma bayan yaƙin.

Wakilin Waliyyul Faƙih a lardin Kermanshah ya kuma yi nuni da saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran kan Makon Kariya Mai Tsarki, yana mai jaddada muhimmancin nazari da fahimtar muhimman saƙonnin dabarun da ke cikinsa.

Ya ce maƙiya suna ƙoƙarin haifar da ruɗani ta hanyar yaɗa bayanai da matsaya masu saɓani, domin su rikita tunanin jama’a da kuma ɓangaren da suke fuskanta.

Hujjatul Islam wal Muslimin Ghafouri ya kuma yi magana kan halin da Amurka ke ciki, yana mai cewa ƙasar tana fuskantar matsaloli da matsin lamba daban-daban. Ya ce ficewar Amurka daga Iraki da Afghanistan ta nuna cewa tsayin dakan al’umma na iya tilasta wa manyan ƙasashen waje barin ƙasashen da suka shiga.

Ya ƙara da cewa Iran tana da isassun damammaki da ƙarfin da za ta iya fuskantar barazanar maƙiya, kuma idan maƙiya suka ɗauki matakin kai hari, Iran za ta iya mayar da martani mai ƙarfi da zai hana sake maimaita irin wannan mataki.

A wani ɓangare na jawabinsa, Limamin Juma’ar Kermanshah ya yi ishara da ikirarin da ake yi kan durƙushewar tattalin arzikin Iran, inda ya yi watsi da waɗannan ikirare-ikirare, yana mai cewa tattalin arzikin Iran ya samu ci gaba tsawon shekaru kuma ƙasar tana da manyan damammaki na tattalin arziki.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha